Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Ministan ya bayyana haka a ranar Jumma’a a lokacinda yake halattar taron watanni uku-uku na majalisar kiwon lafiya ta kasa a Abuja.
Manufar taron na kwanaki biyu dai ita ce tattauna yadda za’a karfafa bangaren lafiya a yankunan karkara na kasar.
Danga karshe ministan ya bayyana cewa Naigeriya ba ta da likitoci a mafi yawan yankunan karkarar kasar, don mafi yawan mutane suna zama a birnin ne. Don haka a halin yanzu a duk fadin kasar ana da likitoci kimani 4000 ne.
Ya ce jami’o’in gwamnati ne kawai suke da asbitocin koyarwa, don haka jami’o’i masu zaman kansa ba sa samar da likitoci a halin yanzun.
342/